Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa zã su ce maka, "Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara." Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: "To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa."