Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a, Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma.