Kuma Shaiɗan ya ce a lõkacin da aka ƙãre al'amarin, "Lalle ne Allah Ya yi muku wa'adi, wa'adin gaskiyã, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na sãɓã muku. Kuma bãbu wani dalĩli a gare ni a kanku fãce na kirã ku, sa'an nan kun karɓã mini. Sabõda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba, kuma ba ku zama mãsu amfãnĩna ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗã ni da shi gabanin wannan (matsayi). Lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi."