23وَأُدخِلَ الَّذينَ آمَنوا وَعَمِلُوا الصّالِحاتِ جَنّاتٍ تَجري مِن تَحتِهَا الأَنهارُ خالِدينَ فيها بِإِذنِ رَبِّهِم ۖ تَحِيَّتُهُم فيها سَلامٌAbubakar GumiKuma aka shigar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwamã a cikinsu da iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta "Salãm", (wãtau Aminci).