Kuma suka bayyana ga Allah gabã daya, sai mãsu rauni suka ce wa waɗanda suka kangara, "Lalle ne mũ, mun kasance mãsu bi a gare ku, to, shin, kũ mãsu kãrewa ga barinmu ne daga azãbar Allah daga wani abu?" Suka ce: "Dã Allah Ya shiryar da mu, dã mun shiryar da ku, daidai ne a kanmu, mun yi rãki ko mun yi haƙuri ba mu da wata mafaka."