9إِنَّما يَنهاكُمُ اللَّهُ عَنِ الَّذينَ قاتَلوكُم فِي الدّينِ وَأَخرَجوكُم مِن دِيارِكُم وَظاهَروا عَلىٰ إِخراجِكُم أَن تَوَلَّوهُم ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم فَأُولٰئِكَ هُمُ الظّالِمونَAbubakar GumiAllah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai.