Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845. Kuna jẽfa sõyayya zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.