2الَّذينَ يُظاهِرونَ مِنكُم مِن نِسائِهِم ما هُنَّ أُمَّهاتِهِم ۖ إِن أُمَّهاتُهُم إِلَّا اللّائي وَلَدنَهُم ۚ وَإِنَّهُم لَيَقولونَ مُنكَرًا مِنَ القَولِ وَزورًا ۚ وَإِنَّ اللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفورٌAbubakar GumiWaɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.