Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi."