105يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا عَلَيكُم أَنفُسَكُم ۖ لا يَضُرُّكُم مَن ضَلَّ إِذَا اهتَدَيتُم ۚ إِلَى اللَّهِ مَرجِعُكُم جَميعًا فَيُنَبِّئُكُم بِما كُنتُم تَعمَلونَAbubakar GumiYã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.