2يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا لا تَرفَعوا أَصواتَكُم فَوقَ صَوتِ النَّبِيِّ وَلا تَجهَروا لَهُ بِالقَولِ كَجَهرِ بَعضِكُم لِبَعضٍ أَن تَحبَطَ أَعمالُكُم وَأَنتُم لا تَشعُرونَAbubakar GumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.