Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce: "Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan.