12۞ اللَّهُ الَّذي سَخَّرَ لَكُمُ البَحرَ لِتَجرِيَ الفُلكُ فيهِ بِأَمرِهِ وَلِتَبتَغوا مِن فَضلِهِ وَلَعَلَّكُم تَشكُرونَAbubakar GumiAllah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde.