11هٰذا هُدًى ۖ وَالَّذينَ كَفَروا بِآياتِ رَبِّهِم لَهُم عَذابٌ مِن رِجزٍ أَليمٌAbubakar GumiWannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi.