24۞ قالَ أَوَلَو جِئتُكُم بِأَهدىٰ مِمّا وَجَدتُم عَلَيهِ آباءَكُم ۖ قالوا إِنّا بِما أُرسِلتُم بِهِ كافِرونَAbubakar Gumi(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."