14وَمَن يَعصِ اللَّهَ وَرَسولَهُ وَيَتَعَدَّ حُدودَهُ يُدخِلهُ نارًا خالِدًا فيها وَلَهُ عَذابٌ مُهينٌAbubakar GumiKuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa.