13تِلكَ حُدودُ اللَّهِ ۚ وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَرَسولَهُ يُدخِلهُ جَنّاتٍ تَجري مِن تَحتِهَا الأَنهارُ خالِدينَ فيها ۚ وَذٰلِكَ الفَوزُ العَظيمُAbubakar GumiWaɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.