56قالَ بَل رَبُّكُم رَبُّ السَّماواتِ وَالأَرضِ الَّذي فَطَرَهُنَّ وَأَنا عَلىٰ ذٰلِكُم مِنَ الشّاهِدينَAbubakar GumiYa ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka."