111وَقُلِ الحَمدُ لِلَّهِ الَّذي لَم يَتَّخِذ وَلَدًا وَلَم يَكُن لَهُ شَريكٌ فِي المُلكِ وَلَم يَكُن لَهُ وَلِيٌّ مِنَ الذُّلِّ ۖ وَكَبِّرهُ تَكبيرًاAbubakar GumiKuma ka ce: "Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba." Kuma ka girmama Shi, girmamãwa.