88۞ قالَ المَلَأُ الَّذينَ استَكبَروا مِن قَومِهِ لَنُخرِجَنَّكَ يا شُعَيبُ وَالَّذينَ آمَنوا مَعَكَ مِن قَريَتِنا أَو لَتَعودُنَّ في مِلَّتِنا ۚ قالَ أَوَلَو كُنّا كارِهينَAbubakar GumiMashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?"