51الَّذينَ اتَّخَذوا دينَهُم لَهوًا وَلَعِبًا وَغَرَّتهُمُ الحَياةُ الدُّنيا ۚ فَاليَومَ نَنساهُم كَما نَسوا لِقاءَ يَومِهِم هٰذا وَما كانوا بِآياتِنا يَجحَدونَAbubakar Gumi"Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu.