Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."