Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne."