Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.