Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.