145وَكَتَبنا لَهُ فِي الأَلواحِ مِن كُلِّ شَيءٍ مَوعِظَةً وَتَفصيلًا لِكُلِّ شَيءٍ فَخُذها بِقُوَّةٍ وَأمُر قَومَكَ يَأخُذوا بِأَحسَنِها ۚ سَأُريكُم دارَ الفاسِقينَAbubakar GumiKuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai."