129قالوا أوذينا مِن قَبلِ أَن تَأتِيَنا وَمِن بَعدِ ما جِئتَنا ۚ قالَ عَسىٰ رَبُّكُم أَن يُهلِكَ عَدُوَّكُم وَيَستَخلِفَكُم فِي الأَرضِ فَيَنظُرَ كَيفَ تَعمَلونَAbubakar GumiSuka ce: "An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa."