Kuma waɗanda suka yanke ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa.