10أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم عَذابًا شَديدًا ۖ فَاتَّقُوا اللَّهَ يا أُولِي الأَلبابِ الَّذينَ آمَنوا ۚ قَد أَنزَلَ اللَّهُ إِلَيكُم ذِكرًاAbubakar GumiAllah Ya yi musu tattalin wata azãba mai tsanani. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abũta hankula, waɗanda suka yi ĩmãni! Haƙĩƙa Allah Ya saukar da wata tunãtarwa zuwa gare ku.