14يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا إِنَّ مِن أَزواجِكُم وَأَولادِكُم عَدُوًّا لَكُم فَاحذَروهُم ۚ وَإِن تَعفوا وَتَصفَحوا وَتَغفِروا فَإِنَّ اللَّهَ غَفورٌ رَحيمٌAbubakar GumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.