Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai."