Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lõkacin da suka ce: "Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kunã sanya shi takardu, kũna bayyana su, kuma kunã ɓõye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah," sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã.