Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.