68وَإِذا رَأَيتَ الَّذينَ يَخوضونَ في آياتِنا فَأَعرِض عَنهُم حَتّىٰ يَخوضوا في حَديثٍ غَيرِهِ ۚ وَإِمّا يُنسِيَنَّكَ الشَّيطانُ فَلا تَقعُد بَعدَ الذِّكرىٰ مَعَ القَومِ الظّالِمينَAbubakar GumiKuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai.