Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.