9يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا إِذا تَناجَيتُم فَلا تَتَناجَوا بِالإِثمِ وَالعُدوانِ وَمَعصِيَتِ الرَّسولِ وَتَناجَوا بِالبِرِّ وَالتَّقوىٰ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذي إِلَيهِ تُحشَرونَAbubakar GumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan za ku yi gãnãwa, to, kada ku gãna game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma ku yi gãnãwa game da alhẽri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda zã a tattara ku zuwa gare, shi.