Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.