53وَيَقولُ الَّذينَ آمَنوا أَهٰؤُلاءِ الَّذينَ أَقسَموا بِاللَّهِ جَهدَ أَيمانِهِم ۙ إِنَّهُم لَمَعَكُم ۚ حَبِطَت أَعمالُهُم فَأَصبَحوا خاسِرينَAbubakar GumiKuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?" Ayyukansu sun ɓãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra.