9قُل ما كُنتُ بِدعًا مِنَ الرُّسُلِ وَما أَدري ما يُفعَلُ بي وَلا بِكُم ۖ إِن أَتَّبِعُ إِلّا ما يوحىٰ إِلَيَّ وَما أَنا إِلّا نَذيرٌ مُبينٌAbubakar GumiKa ce: "Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da ni kõ game da ku (na gaibi) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa."