Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."