66۞ قُل إِنّي نُهيتُ أَن أَعبُدَ الَّذينَ تَدعونَ مِن دونِ اللَّهِ لَمّا جاءَنِيَ البَيِّناتُ مِن رَبّي وَأُمِرتُ أَن أُسلِمَ لِرَبِّ العالَمينَAbubakar GumiKa ce: "Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu."