39هُوَ الَّذي جَعَلَكُم خَلائِفَ فِي الأَرضِ ۚ فَمَن كَفَرَ فَعَلَيهِ كُفرُهُ ۖ وَلا يَزيدُ الكافِرينَ كُفرُهُم عِندَ رَبِّهِم إِلّا مَقتًا ۖ وَلا يَزيدُ الكافِرينَ كُفرُهُم إِلّا خَسارًاAbubakar GumiShĩ ne Wanda Ya sanya ku mãsu maye wa junã, a cikin ƙasã. To, wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa yanã a kansa. Kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme fãce baƙin jini, kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme face hasãra.