29إِنَّ الَّذينَ يَتلونَ كِتابَ اللَّهِ وَأَقامُوا الصَّلاةَ وَأَنفَقوا مِمّا رَزَقناهُم سِرًّا وَعَلانِيَةً يَرجونَ تِجارَةً لَن تَبورَAbubakar GumiLalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro.