24إِنّا أَرسَلناكَ بِالحَقِّ بَشيرًا وَنَذيرًا ۚ وَإِن مِن أُمَّةٍ إِلّا خَلا فيها نَذيرٌAbubakar GumiLalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta.