22وَلَمّا رَأَى المُؤمِنونَ الأَحزابَ قالوا هٰذا ما وَعَدَنَا اللَّهُ وَرَسولُهُ وَصَدَقَ اللَّهُ وَرَسولُهُ ۚ وَما زادَهُم إِلّا إيمانًا وَتَسليمًاAbubakar GumiKuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da ManzonSa suka yi mana wa'adi, Allah da ManzonSa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa.