68إِنَّ أَولَى النّاسِ بِإِبراهيمَ لَلَّذينَ اتَّبَعوهُ وَهٰذَا النَّبِيُّ وَالَّذينَ آمَنوا ۗ وَاللَّهُ وَلِيُّ المُؤمِنينَAbubakar GumiLalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a (zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma Allah ne Majiɓincin mũminai.