184فَإِن كَذَّبوكَ فَقَد كُذِّبَ رُسُلٌ مِن قَبلِكَ جاءوا بِالبَيِّناتِ وَالزُّبُرِ وَالكِتابِ المُنيرِAbubakar GumiTo, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske.