Ya ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?