Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku, gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali.