Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.